Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 23:20-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. “Ni da kaina zan aiki mala'ika a gabanku don ya kiyaye ku a sa'ad da kuke tafiya, ya kuma kai ku inda na shirya muku.

21. Ku nuna masa bangirma, ku kasa kunne ga maganarsa. Kada ku tayar masa, gama ba zai gafarta muku laifofinku ba, gama shi wakilina ne.

22. Idan kun kasa kunne a hankali ga maganarsa, kuka aikata dukan abin da na faɗa, sai in zama maƙiyin maƙiyanku da magabcin magabtanku.

23. Mala'ikana zai wuce gabanku, ya bi da ku inda Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Kan'aniyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa suke, zan kuma hallakar da su ƙaƙaf.

24. Ba za ku rusuna wa allolinsu ba, balle fa ku bauta musu, kada ku yi yadda suke yi. Sai ku hallaka allolinsu ɗungum, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu.

25. Za ku bauta wa Ubangiji Allahnku, ni kuwa zan yalwata abincinku da ruwan shanku, in kuma kawar muku da ciwo.

26. A ƙasarku, mace ba za ta yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai.

27. “Zan aiki razanata a gabanku, in sa mutanen da za ku gamu da su su ruɗe. Zan sa maƙiyanku duka su ba ku baya, su sheƙa a guje.

28. Zan aiki zirnako a gabanku, su kore muku Hiwiyawa, da Kan'aniyawa, da Hittiyawa.

29. Ba a shekara guda zan kore muku su ba, don kada ƙasar ta zama kufai har namomin jeji su fi ƙarfinku.

30. Da kaɗan da kaɗan zan kore muku su, har yawanku ya kai yadda za ku mallaki ƙasar.

31. Zan yanka muku kan iyaka daga Bahar Maliya zuwa tekun Filistiyawa, daga jeji kuma zuwa Kogin Yufiretis. Gama zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kore su daga gabanku.

32. Kada ku ƙulla alkawari da su, ko da allolinsu.

Karanta cikakken babi Fit 23