Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 18:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yetro, firist na Madayana, surukin Musa, ya ji dukan abin da Allah ya yi wa jama'arsa, wato Musa da Isra'ilawa, yadda Ubangiji ya fito da su daga Masar.

2. Ya kawo Ziffora matar Musa, wadda Musa ya aika da ita gida.

3. Yetro kuma ya kawo 'ya'yanta biyu maza, Gershom da Eliyezer tare da ita. Gama Musa ya ce, “Ni baƙo ne a baƙuwar ƙasa.” Saboda haka ne ya raɗa wa ɗaya daga cikin 'ya'yansa, suna, Gershom.

4. Ya kuma ce, “Allah na ubanan shi ne ya taimake ni, ya cece ni daga takobin Fir'auna,” saboda haka ya raɗa wa ɗayan, suna, Eliyezer.

5. Sai Yetro ya kawo wa Musa 'ya'yansa maza da matarsa a cikin jeji inda suka yi zango kusa da dutsen Allah.

6. Aka faɗa wa Musa, “Ga surukinka, Yetro, yana zuwa wurinka da matarka da 'ya'yanta biyu tare da ita.”

7. Musa kuwa ya fita ya marabce shi, ya sunkuya, ya sumbace shi. Suka gaisa, suka tambayi lafiyar juna, sa'an nan suka shiga alfarwa.

Karanta cikakken babi Fit 18