Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 16:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Musa ya ce wa Haruna, “Faɗa wa taron jama'ar Isra'ila, su matso nan a gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninsu.”

10. Sa'ad da Haruna yake magana da taron jama'ar, suka duba wajen jeji, sai ga ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a cikin girgije.

11. Ubangiji kuwa ya yi magana da Musa ya ce,

12. “Na ji gunagunin Isra'ilawa, amma ka faɗa musu cewa, ‘A tsakanin faɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe za ku kuma ƙoshi da abinci. Sa'an nan za ku sani, ni Ubangiji Allahnku ne.”’

13. Da maraice makware suka zo suka rufe zangon, da safe kuma raɓa ta kewaye zangon.

14. Sa'ad da raɓar ta kaɗe, sai ga wani abu tsaki-tsaki mai laushi, fari, kamar hazo a ƙasa.

15. Sa'ad da Isra'ilawa suka gan shi, suka ce wa junansu, “Manna,” wato “Mece ce wannan?” Gama ba su san irinta ba.Musa kuwa ya ce musu, “Wannan ita ce abincin da Ubangiji ya ba ku, ku ci.

16. Abin da Ubangiji ya umarta ke nan, kowannenku ya tattara wadda ta ishe shi ci, kowa ya sami mudu daidai bisa ga yawan mutanen da yake cikin kowace alfarwa.”

17. Isra'ilawa suka yi haka nan, suka tattara, waɗansu suka zarce, waɗansu kuma ba su kai ba.

18. Amma da aka auna da mudu, ta waɗanda suka zarce ba ta yi saura ba, ta waɗanda ba su kai ba, ba ta gaza ba. Kowane mutum ya tattara daidai cinsa.

Karanta cikakken babi Fit 16