Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 12:40-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

40. Zaman da Isra'ilawa suka yi a Masar shekara ce arbaminya da talatin.

41. A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar.

42. Daren nan da Ubangiji ya sa domin ya fito da Isra'ilawa daga ƙasar Masar, daren ne wanda wajibi ne Isra'ilwa su kiyaye domin su girmama Ubangiji dukan zamanansu.

43. Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Wannan ita ce ƙa'idar Idin Ƙetarewa, baƙo ba zai ci ba.

44. Amma kowane bawa da aka saya da kuɗi ya iya ci, in dai an yi masa kaciya.

45. Amma da baƙo da wanda aka yi ijararsa ba zai ci shi ba.

46. A gidan da aka shirya, nan za a ci, kada a fitar da naman waje, kada kuma a karye ƙashinsa.

47. Dukan taron jama'ar Isra'ila za su kiyaye Idin Ƙetarewa.

48. Idan baƙon da yake zaune tare da ku yana so ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji tare da ku, to, sai a yi wa kowane namiji da yake a gidansa kaciya sa'an nan ya iya shiga idin, shi kuma ya zama ɗan ƙasa. Daɗai, marar kaciya ba zai ci ba.

49. Wannan ka'ida ta shafi ɗan ƙasa daidai da baƙon da yake baƙunci tsakaninku.”

Karanta cikakken babi Fit 12