Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 12:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna cikin ƙasar Masar,

2. wannan wata zai zama wata na farko a shekara a gare su.

3. A faɗa wa dukan taron Isra'ilawa cewa, “A rana ta goma ga watan nan, kowane namiji ya ɗauki ɗan rago ko ɗan akuya daga cikin garke domin iyalinsa, dabba ɗaya domin kowane gida.

4. Idan da wanda iyalinsa ba za su iya cinye dabba guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki dabba guda gwargwadon yawansu.

5. Tilas ne dabbar ta kasance lafiyayyiya ƙalau, bana ɗaya. Za ku kamo daga cikin tumakinku ko awaki.

6. Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato sa'ad da dukan taron jama'ar Isra'ila za su yanka ragunansu da maraice.

7. Sa'an nan ku ɗibi jinin, ku sa a dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar gidajen da za a ci naman dabbobin.

8. A daren nan za ku gasa naman, ku ci da abinci marar yisti, da ganyaye masu ɗaci.

9. Kada ku ci shi ɗanye ko daffaffe da ruwa, amma a gasa shi, da kan, da ƙafafun, da kayan cikin.

10. Kada ku bar kome ya kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi.

11. Ga yadda za ku ci shi, da ɗamara a gindinku, da takalma a ƙafafunku, da sanda a hannunku, da gaggawa kuma za ku ci shi. Idin Ƙetarewa ne ga Ubangiji.

12. A daren nan zan ratsa ƙasar Masar, in bugi kowane ɗan fari na ƙasar, na mutum da na dabba. Zan hukunta gumakan Masar duka, gama ni ne Ubangiji.

13. Jinin da yake bisa gidajenku zai nuna inda kuke. Sa'ad da na ga jinin zan tsallake ku, ba kuma wani bala'in da zai same ku, ya hallaka ku, a lokacin da zan bugi ƙasar Masar.

Karanta cikakken babi Fit 12