Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 10:9-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Musa ya amsa, “Da samarinmu, da tsofaffinmu za mu tafi, da 'ya'yanmu mata da maza za su fita tare da mu, da kuma garkunanmu da shanunmu, gama wajibi ne mu yi idi a gaban Ubangiji.

10. Fir'auna ya ce musu, “To, Ubangiji ya taimaka bisa ga niyyarku, amma matanku da ƙanananku ba za su tafi ba, gama kuna da niyyar mugunta a zuciyarku.

11. Sai dai ku mazaje, ku tafi ku bauta wa Ubangiji, gama abin da kuke so ke nan.” To, aka kore su daga gaban Fir'auna.

12. Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa ƙasar Masar domin fara ta zo. Farar kuwa za ta rufe ƙasar Masar, ta cinye duk tsire-tsire da ganyayen da suke cikin ƙasar, da iyakar abin da ƙanƙara ta rage.”

13. Sai Musa ya miƙa sandansa bisa ƙasar Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a ƙasar dukan yini da dukan dare, har safiya. Iskar gabas ɗin kuwa ta kawo farar.

14. Farar ta mamaye ƙasar Masar, ta rufe dukan ƙasar. Ba a taɓa ganin fara ta taru da yawa kamar haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin kamar haka ba.

15. Ta rufe dukan fuskar ƙasa har ƙasar ta yi duhu. Ta cinye kowane tsiro na ƙasar da dukan 'ya'yan itatuwa waɗanda ƙanƙara ta rage. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar.

16. Fir'auna ya aika da gaggawa a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku.

17. Amma ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma roƙar mini Ubangiji Allahnku ya ɗauke mini wannan mutuwa.”

18. Sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna, ya tafi ya roƙi Ubangiji.

19. Ubangiji kuwa ya sa iska mai ƙarfi ta huro daga wajen yamma, ta kwashi farar, ta zuba ta a Bahar Maliya. Ko fara guda ba ta ragu a cikin iyakar Masar ba.

20. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, Fir'auna kuwa ya ƙi sakin Isra'ilawa.

21. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama, domin a yi duhu cikin ƙasar Masar, irin duhun da za a iya taɓawa.”

22. Sai Musa ya miƙa hannunsa sama, aka kuwa yi duhu baƙi ƙirin har kwana uku a dukan ƙasar Masar.

23. Mutum bai iya ganin ɗan'uwansa ba, ba kuma mutumin da ya iya fita gidansa har kwana uku. Amma akwai haske inda Isra'ilawa suke zaune.

24. Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna ya ce musu, “Ku tafi ku bauta wa Ubangiji, sai dai ku bar tumakinku, da awakinku, da shanunku a nan, amma ku ku tafi da 'ya'yanku.”

25. Musa kuwa ya ce, “In haka ne, kai ka ba mu abin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu hadayu da su.

26. Don haka sai mu tafi da dabbobinmu, ko kofato ba za a bari a baya ba, gama daga cikinsu ne za mu ɗibi abin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu. Ba mu kuma san irin abin da za mu miƙa wa Ubangiji ba, sai mun kai can.”

27. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna har bai yarda ya sake su ba.

Karanta cikakken babi Fit 10