Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 10:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Je ka wurin Fir'auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da ta fādawansa domin in aikata waɗannan mu'ujizai nawa a tsakiyarsu,

2. domin kuma ka sanar da 'ya'yanka da jikokinka yadda na shashantar da Masarawa, na kuma aikata waɗannan mu'ujizai a tsakiyarsu. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.”

3. Saboda haka Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi yarda ka ba da kanka a gare ni? Saki jama'ata don su tafi su yi mini sujada.

4. In kuwa ka ƙi yarda ka bar jama'ata su tafi, to, gobe zan aiko da fara cikin ƙasarka,

5. za ta rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za ta cinye sauran abin da ya kuɓuta daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a ƙasar.

6. Za su cika fādarka, da dukan gidajen fādawanka, da na dukan Masarawa. Iyayenka da kakanninka ba su taɓa ganin irin faran nan ba, tun daga ran da suke ƙasar, har wa yau.”’ Sai ya juya ya fita daga gaban Fir'auna.

7. Fādawan Fir'auna kuwa suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai riƙa jawo mana masifa? Ka saki mutanen, su fita su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Ashe, har yanzu ba ka sani Masar ta lalace ba?”

Karanta cikakken babi Fit 10