Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 9:17-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawari wanda na kafa tsakanina da dukan talikan da suke bisa duniya.”

18. 'Ya'yan Nuhu waɗanda suka fito daga jirgi su ne Shem, da Ham, da Yafet. Ham shi ne mahaifin Kan'ana.

19. Su uku ɗin nan su ne 'ya'yan Nuhu, daga gare su duniya za ta cika da mutane.

20. Nuhu shi ya fara noma, ya yi gonar inabi.

21. Ya sha daga cikin ruwan inabin ya kuwa bugu, ya kwanta tsirara a cikin alfarwarsa.

22. Sai Ham, mahaifin Kan'ana, ya ga tsiraicin mahaifinsa, ya faɗa wa 'yan'uwansa biyu waɗanda suke waje.

23. Sai Shem da Yafet suka ɗauki riga, suka ɗibiya bisa kafaɗunsu, suka yi tafiya da baya da baya suka rufa tsiraicin mahaifinsu, suka juya fuskokinsu, ba su kuwa ga tsiraicin mahaifinsu ba.

24. Sa'ad da ruwan inabin ya sau Nuhu, ya san abin da ƙaramin ɗansa ya yi masa.

25. Sai ya ce, “La'ananne ne Kan'ana, bawan bayi zai zama ga 'yan'uwansa.”

Karanta cikakken babi Far 9