Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 9:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Na kafa alkawarina da ku. Daɗai ba za a ƙara hallaka talikai duka da ruwa ba, ba kuma za a ƙara yin Ruwan Tsufana da zai hallaka duniya ba.”

12. Allah ya ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da yake tare da ku, har dukan zamanai masu zuwa,

13. na sa bakana cikin girgije, ya zama alamar alkawari tsakanina da duniya.

14. Sa'ad da na kawo gizagizai bisa duniya, aka ga bakan a cikin gizagizai,

15. zan tuna da alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da dukan talikai. Ruwa kuma ba zai ƙara yin rigyawar da za ta hallaka talikai duka ba.

16. Sa'ad da bakan yake cikin girgije zan dube shi, in tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da kowane mai rai da dukan talikan da suke bisa duniya.”

17. Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawari wanda na kafa tsakanina da dukan talikan da suke bisa duniya.”

18. 'Ya'yan Nuhu waɗanda suka fito daga jirgi su ne Shem, da Ham, da Yafet. Ham shi ne mahaifin Kan'ana.

19. Su uku ɗin nan su ne 'ya'yan Nuhu, daga gare su duniya za ta cika da mutane.

20. Nuhu shi ya fara noma, ya yi gonar inabi.

21. Ya sha daga cikin ruwan inabin ya kuwa bugu, ya kwanta tsirara a cikin alfarwarsa.

22. Sai Ham, mahaifin Kan'ana, ya ga tsiraicin mahaifinsa, ya faɗa wa 'yan'uwansa biyu waɗanda suke waje.

Karanta cikakken babi Far 9