Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 8:4-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ya zama kuwa a ran sha bakwai ga wata na bakwai, sai jirgin ya tafi ya tsaya bisa kan dutsen Ararat.

5. Ruwa ya yi ta raguwa har wata na goma. A ran ɗaya ga wata na goma, sai kawunan duwatsu suka ɓullo.

6. A ƙarshen kwana arba'in Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi,

7. sai ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har lokacin da ruwan ya ƙafe a duniya.

8. Sai kuma ya aiki kurciya ta gani ko ruwa ya janye,

9. amma kurciyar ba ta sami inda za ta sauka ba, sai ta komo wurinsa cikin jirgi, gama har yanzu ruwa na rufe ƙasa duka. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauko ta ya shigar da ita cikin jirgi tare da shi.

10. Ya jira kuma har kwana bakwai, sai kuma ya sāke aiken kurciyar daga cikin jirgin.

11. Kurciyar kuwa ta komo wurinsa da maraice, ga shi kuwa, a bakinta sabon tohon zaitun wanda ta tsinko, domin haka Nuhu ya gane ruwa ya janye daga duniya.

12. Sai ya sāke dakatawa har kwana bakwai, ya kuma aiki kurciya, amma ba ta ƙara komowa wurinsa ba.

13. A rana ta fari ga wata na fari na shekara ta ɗari shida da ɗaya na Nuhu, ruwa ya ƙafe a duniya. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya duba, sai ga ƙasa busasshiya.

14. Ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, duniya ta bushe.

15. Sa'an nan sai Allah ya ce wa Nuhu,

16. “Fito daga cikin jirgi, kai da matarka, da 'ya'yanka da matan 'ya'yanka tare da kai.

17. Ka fito da kowane abu mai rai tare da kai, dukan talikai, wato tsuntsaye, da dabbobi, da kowane abu mai rarrafen da yake rarrafe bisa ƙasa, domin su hayayyafa su kuma riɓaɓɓanya a duniya.”

18. Sai Nuhu ya fito, da 'ya'yansa, da matarsa da matan 'ya'yansa tare da shi,

Karanta cikakken babi Far 8