Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 8:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. A rana ta fari ga wata na fari na shekara ta ɗari shida da ɗaya na Nuhu, ruwa ya ƙafe a duniya. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya duba, sai ga ƙasa busasshiya.

14. Ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, duniya ta bushe.

15. Sa'an nan sai Allah ya ce wa Nuhu,

16. “Fito daga cikin jirgi, kai da matarka, da 'ya'yanka da matan 'ya'yanka tare da kai.

17. Ka fito da kowane abu mai rai tare da kai, dukan talikai, wato tsuntsaye, da dabbobi, da kowane abu mai rarrafen da yake rarrafe bisa ƙasa, domin su hayayyafa su kuma riɓaɓɓanya a duniya.”

18. Sai Nuhu ya fito, da 'ya'yansa, da matarsa da matan 'ya'yansa tare da shi,

19. da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abin da yake motsi a bisa duniya, suka fito daga jirgi ɗaki ɗaki bisa ga irinsu.

20. Nuhu ya gina wa Ubangiji bagade, ya ɗiba daga cikin kowace irin dabba mai tsarki, da kowane tsuntsu mai tsarki, ya miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden.

21. Sa'ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, “Ba zan ƙara la'anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā.

22. Muddin duniya tana nan, lokacin shuka da lokacin girbi, damuna da rani, yini da dare, ba za su daina ba.”

Karanta cikakken babi Far 8