Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 7:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Ubangiji ya ce wa Nuhu, “Ka shiga jirgin, kai da iyalinka duka, gama na ga a wannan zamani, kai adali ne a gare ni.

2. Daga cikin dabbobi masu tsarki ka ɗauki bakwai bakwai, namiji da ta mace, marasa tsarki kuwa namiji da ta mace,

3. da kuma tsuntsayen sararin sama bakwai bakwai, namiji da ta mace, domin a wanzar da irinsu a duniya duka.

4. Gama da sauran kwana bakwai kāna in sa a yi ruwa a duniya yini arba'in da dare arba'in. Dukan abu mai rai wanda na yi zan shafe shi daga duniya.”

5. Nuhu kuwa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.

6. Nuhu yana da shekara ɗari shida lokacin da Ruwan Tsufana ya kwararo bisa duniya.

7. Nuhu da 'ya'yansa da matarsa, da matan 'ya'yansa tare da shi suka shiga jirgi, domin su tsira daga Ruwan Tsufana.

8. Daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da na tsuntsaye, da na kowane mai rarrafe a ƙasa,

9. biyu biyu, namiji da mata, suka shiga jirgi tare da Nuhu, kamar yadda Allah ya umarci Nuhu.

10. Sai bayan kwana bakwai ruwayen suka kwararo bisa duniya.

11. A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.

12. Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya yini arba'in da dare arba'in.

13. A wannan rana Nuhu da 'ya'yansa, Shem, da Ham, da Yafet, da matar Nuhu da matan 'ya'yansa tare suka shiga jirgin,

14. su da kowace dabbar jeji bisa ga irinta, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowane mai rarrafe wanda yake rarrafe bisa ƙasa, bisa ga irinsa, da kowane tsuntsun gida da na jeji wanda yake numfashi.

Karanta cikakken babi Far 7