Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 50:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. gama 'ya'yansa suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan'ana, suka kuwa binne shi a kogon da yake saurar Makfela a gabashin Mamre, wanda Ibrahim ya saya, duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta.

14. Bayan da Yusufu ya binne mahaifinsa, ya koma Masar tare da 'yan'uwansa da dukan waɗanda suka tafi tare da shi don jana'izar mahaifinsa.

15. Sa'ad da 'yan'uwan Yusufu suka ga mahaifinsu ya rasu, suka ce, “Mai yiwuwa ne Yusufu zai ƙi jininmu, ya sāka mana dukan muguntar da muka yi masa.”

16. Saboda haka suka aika wa Yusufu da jawabi, suka ce, “Mahaifinka ya ba da wannan umarni kafin rasuwarsa,

17. ya ce, ‘Ku faɗa wa Yusufu, ina roƙonsa, ya gafarta laifin 'yan'uwansa da zunubansu, gama sun yi masa mugunta.’ Yanzu fa, muna roƙonka, ka gafarta laifofin bayin Allah na mahaifinka.” Yusufu ya yi kuka sa'ad da suka yi magana da shi.

18. 'Yan'uwansa kuma suka zo suka fāɗi a gabansa, suka ce, “Ga shi, mu barorinka ne.”

19. Amma Yusufu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ni ba a matsayin Allah nake ba.

20. A nufinku mugunta ce kuka yi mini, amma Allah ya maishe ta alheri, don a rayar da jama'a masu yawa waɗanda suke da rai a yau.

21. Don haka kada ku ji tsoro, zan tanada muku, ku da ƙanananku.” Ta haka ya ta'azantar da su, ya yi musu magana ta kwantar da zuciya.

22. Haka fa Yusufu ya zauna a Masar, shi da iyalin gidan mahaifinsa. Yusufu kuwa ya yi shekara ɗari da goma a duniya.

23. Yusufu fa ya ga 'ya'yan Ifraimu har tsara ta uku, aka kuma haifi 'ya'yan Makir ɗan Manassa, aka karɓe su cikin iyalin Yusufu.

24. Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”

Karanta cikakken babi Far 50