Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 45:10-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Za ka zauna a ƙasar Goshen, za ka zauna kusa da ni, kai da 'ya'yanka da jikokinka, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunanka na shanu, da dukan abin da kake da shi.

11. A nan zan cishe ka, gama akwai sauran shekara biyar masu zuwa na yunwa, don kada ka tsiyace, kai da iyalinka, da duk wanda yake tare da kai.’ ”

12. Yanzu, da idanunku kun gani, idanun ɗan'uwana Biliyaminu kuma sun gani, cewa bakina ne yake magana da ku.

13. Ku faɗa wa mahaifina dukan darajar da nake da ita a Masar da dukan abin da kuka gani. Ku gaggauta ku gangaro mini da mahaifina a nan.”

14. Sai Yusufu ya rungumi ɗan'uwansa Biliyaminu ya yi ta kuka, Biliyaminu ma ya yi kuka a bisa kafaɗun Yusufu.

15. Ya sumbaci 'yan'uwansa duka, ya yi kuka bisansu, bayan wannan sai 'yan'uwansa suka yi taɗi da shi.

16. Sa'ad da labari ya kai gidan Fir'auna cewa, “'Yan'uwan Yusufu sun zo,” abin ya yi wa Fir'auna da fādawansa daɗi ƙwarai.

17. Sai Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ka faɗa wa 'yan'uwanka su yi wannan, ‘Ku yi wa dabbobinku laftu ku koma a ƙasar Kan'ana.

18. Ku ɗauko mahaifinku da iyalanku, ku zo wurina, ni kuwa zan ba ku yankin ƙasa mafificiya a Masar, za ku ci moriyar ƙasar.’

19. Ka kuma umarce su ka ce, ‘Ku ɗauki kekunan shanu daga ƙasar Masar domin 'yan ƙanananku da matanku, ku ɗauko mahaifinku, ku zo.

20. Kada ku damu da kayayyakinku, gama abin da yake mafi kyau duka a ƙasar Masar naku ne.’ ”

21. Haka kuwa 'ya'yan Isra'ila suka yi. Yusufu kuma ya ba su kekunan shanu bisa ga umarnin Fir'auna, ya ba su guzuri don hanya.

Karanta cikakken babi Far 45