Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 44:30-31-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30-31. “Domin haka kuwa, yanzu, idan na koma wurin baranka, mahaifina, ba tare da saurayin ba, in har bai ga yaron tare da ni ba, zai mutu, gama ransa ya shaƙu da saurayin, barorinka kuwa za su sa baranka, mahaifinmu, ya mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa.

32. Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa ya zauna a kaina a gaban mahaifina duka raina.’

33. Domin haka fa, ina roƙonka, bari ni baranka in zama bawa gare ka, shugabana, a maimakon saurayin a bar saurayin ya koma tare da 'yan'uwansa.

34. Gama yaya zan iya komawa wurin mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? Ina jin tsoron ganin ɓarnar da za ta auko wa mahaifina.”

Karanta cikakken babi Far 44