Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 43:19-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Sai suka hau wurin mai hidimar gidan Yusufu, suka yi magana da shi a ƙofar gida,

20. suka ce, “Ya shugaba, mun zo a karo na farko sayen abinci,

21. amma da muka isa zango muka buɗe tayakanmu sai ga kuɗin kowannenmu cif cif bakin taikinsa, don haka ga su a hannunmu, mun sāke komowa da su,

22. ga waɗansu kuɗin kuma mun riƙo a hannunmu, mun gangaro mu ƙara sayen abinci. Ba mu san wanda ya sa kuɗin nan namu a tayakanmu ba.”

23. Ya amsa ya ce, “Salama na tare da ku, kada ku ji tsoro, Allahnku da Allah na mahaifinku ne kaɗai ya sa muku dukiyar cikin tayakanku. Na karɓi kuɗinku.” Sai ya fito musu da Saminu.

24. Da mutumin ya kawo su gidan Yusufu, ya ba su ruwa, suka kuwa wanke ƙafafunsu, sa'an nan kuma ya bai wa jakunansu tauna,

25. sai suka shirya tsarabar, domin Yusufu yana zuwa da tsakar rana, saboda sun ji, wai zai ci abinci a nan.

26. Sa'ad da Yusufu ya koma gida, suka kawo tsarabar da suka riƙo masa cikin gida, suka sunkuya har ƙasa a gabansa.

27. Ya tambayi lafiyarsu ya ce, “Mahaifinku yana lafiya, tsohon nan da kuka yi magana a kansa? Yana nan da rai?”

28. Sai suka amsa, “Bawanka, mahaifinmu yana lafiya, har yanzu yana da rai.” Suka sunkuya suka yi masa mubaya'a.

29. Sai ya ɗaga idanunsa, ya ga ɗan'uwansa Biliyaminu, ɗan da mahaifiyarsa ta haifa, ya ce, “Wannan shi ne auta naku, wanda kuka yi mini magana a kansa? Allah ya yi maka alheri ɗana!”

30. Da Yusufu ya ji kamar zai yi kuka sabili da zuciyarsa tana begen ɗan'uwansa, sai ya gaggauta ya nemi wurin yin kuka. Ya shiga ɗakinsa, a can ya yi kuka.

31. Sa'an nan ya wanke fuskarsa, ya fito ya ɗaure, ya umarta a kawo abinci.

32. Aka hidimta masa shi kaɗai, su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sukan ci abinci tare da Ibraniyawa ba, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa.

33. Aka zaunar da 'yan'uwan Yusufu a gaban Yusufu bisa ga shekarunsu na haihuwa, daga babba zuwa ƙarami. 'Yan'uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki.

34. Daga teburin da yake a gabansa aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Biliyaminu ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.

Karanta cikakken babi Far 43