Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 40:16-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sa'ad da shugaban masu tuya ya ga fassarar tana da kyau, sai ya ce wa Yusufu, “Ni ma cikin nawa mafarki, na ga kwanduna uku na waina a bisa kaina.

17. A kwandon da yake bisa ɗin akwai toye-toye iri iri domin Fir'auna, amma ga tsuntsaye suna ta ci daga cikin kwandon da yake bisa duka, wato wanda yake bisa kaina ɗin.”

18. Yusufu ya amsa, “Wannan ita ce fassararsa, kwandunan uku, kwana uku ne,

19. bayan kwana uku Fir'auna zai falle kanka ya rataye ka a bisa itace, tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.”

20. A rana ta uku, wadda take ranar haihuwar Fir'auna, Fir'auna ya yi wa dukan bayinsa biki, sai ya kawo shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya a gaban fādawansa.

21. Ya komar da shugaban masu shayarwa a matsayinsa na shayarwa, ya kuwa miƙa finjali a hannun Fir'auna,

22. amma ya rataye shugaban masu tuya kamar yadda Yusufu ya fassara musu.

23. Duk da haka shugaban masu shayarwar bai tuna da Yusufu ba, amma ya manta da shi.

Karanta cikakken babi Far 40