Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 4:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Hukuncina ya fi ƙarfina.

14. Ga shi, yanzu ka kore ni a guje daga fuskar ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”

15. Sai Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Wanda duk ya kashe Kayinu, za a rama masa har sau bakwai.” Ubangiji kuma ya sa wa Kayinu tabo, domin duk wanda ya iske shi kada ya kashe shi.

16. Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya zauna a ƙasar Nod, gabashin Aidan.

17. Kayinu ya san matarsa, ta kuwa yi ciki ta haifi Anuhu, ya kuwa gina birni ya sa wa birnin sunan ɗansa, Anuhu.

18. An haifa wa Anuhu ɗa, wato Airad. Airad ya haifi Mehuyayel, Mehuyayel kuwa ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifi Lamek.

19. Lamek ya auri mata biyu, sunan ɗayar Ada, ta biyun kuwa Zulai.

20. Ada ta haifi Yabal, shi ne ya zama uban mazaunan alfarwa, makiyayan dabbobi.

21. Sunan ɗan'uwansa Yubal, wanda ya zama uban makaɗan garaya da mabusan sarewa.

22. Zulai kuwa ta haifi Tubal-kayinu, shi ne asalin maƙeran dukan kayayyakin tagulla da na baƙin ƙarfe. Sunan 'yar'uwar Tubalkayinu Na'ama ne.

Karanta cikakken babi Far 4