Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 34:7-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. 'Ya'yan Yakubu, maza, kuwa sa'ad da suka komo daga saura, da suka ji yadda aka yi, sai suka hasala, abin ya ba su haushi ƙwarai, don Shekem ya yi aikin wauta ga Isra'ila da ya kwana da 'yar Yakubu. Gama irin wannan abu, bai kamata a yi shi ba.

8. Amma Hamor ya yi magana da su, ya ce, “Zuciyar ɗana Shekem tana begen 'yarku, ina roƙonku, ku ba shi ita aure.

9. Ku yi aurayya da mu. Ku ba mu 'yan matanku, ku kuma ku auri 'yan matanmu.

10. Sai ku zauna tare da mu, ƙasar kuma tana gabanku. Ku zauna a cikinta ku yi sana'a, ku sami dukiya.”

11. Shekem kuma ya ce wa mahaifin Dinatu da 'yan'uwanta, “Bari in sami tagomashi a idanunku, dukan abin da kuka ce kuwa, sai in yi.

12. Ku faɗa mini ko nawa ne dukiyar auren da sadakin, zan kuwa bayar bisa ga yadda kuka faɗa mini, in dai kawai ku ba ni budurwar ta zama matata.”

13. 'Ya'yan Yakubu, maza, suka amsa wa Shekem da mahaifinsa Hamor a ha'ince, domin ya ɓata 'yar'uwarsu Dinatu.

14. Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu aurar da 'yar'uwarmu ga marasa kaciya, gama wannan abin kunya ne a gare mu.

15. Ta wannan hali ne kaɗai za mu yarda, wato idan za ku zama kamarmu, ku yi wa dukan mazajenku kaciya.

16. Sa'an nan za mu ba ku auren 'ya'yanmu mata, mu kuma mu auro wa kanmu 'ya'yanku mata. Sai kuwa mu zauna tare da ku, mu zama jama'a ɗaya.

17. Amma idan ba ku saurare mu kun yi kaciya ba, sai mu ɗauki 'yarmu, mu kama hanyarmu.”

18. Hamor da ɗansa Shekem suka yi na'am da sharuɗan.

19. Saurayin kuwa bai yi jinkirin aikata batun ba, gama yana jin daɗin 'yar Yakubu. Shekem kuwa shi ne aka fi darajantawa a cikin gidan.

20. Hamor kuwa da ɗansa Shekem, suka je dandali a bakin ƙofar birni, suka yi wa mutanen birninsu magana, suka ce,

21. “Waɗannan mutane suna abuta da mu, ai, sai su zauna a ƙasar a sake, gama ga shi akwai isasshen fili a ƙasar dominsu. Bari mu auri 'ya'yansu mata, mu kuma mu aurar musu da 'ya'yanmu mata.

22. Ga sharaɗin da mutanen za su yarda su zauna tare da mu, mu zama jama'a ɗaya, wato kowane namiji a cikinmu ya yi kaciya kamar yadda su suke da kaciya.

23. Da shanunsu, da dukiyarsu da dukan dabbobinsu, ashe, ba za su zama namu ba? Bari dai kurum mu yarda da su, su zauna tare da mu.”

24. Duk jama'ar birnin suka yarda da maganar Hamor da ɗansa Shekem. Aka kuwa yi wa kowane namiji kaciya.

25. A rana ta uku, sa'ad da jikunansu suka yi tsami, biyu daga cikin 'ya'yan Yakubu, Saminu da Lawi, 'yan'uwan Dinatu, suka ɗauki takubansu suka fāɗa wa birnin ba labari, suka karkashe mazajen duka.

26. Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dinatu daga gidan Shekem suka yi tafiyarsu.

Karanta cikakken babi Far 34