Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 31:47-55 Littafi Mai Tsarki (HAU)

47. Laban ya sa masa suna Yegar-sahaduta, amma Yakubu ya kira shi Galeyed.

48. Laban ya ce, “Wannan tsibi shaida ce tsakanina da kai yau.” Saboda haka ya sa wa wurin suna Galeyed.

49. Laban kuma ya kira wurin Mizfa, gama ya ce, “Ubangiji ya kiyaye tsakanina da kai sa'ad da muka rabu da juna.

50. Idan ka wulakanta 'ya'yana mata, ko kuma ka auri wata mata banda 'ya'yana mata, ko da yake babu kowa tare da mu, ka tuna, Allah shi ne mashaidi tsakanina da kai.”

51. Sai Laban ya ce wa Yakubu, “Dubi wannan tsibi da al'amudi, wanda na kafa tsakanina da kai.

52. Wannan tsibi, shaida ce, al'amudin kuma shaida ce ba zan zarce wannan tsibi zuwa wurinka ba, kai kuma ba za ka zarce wannan tsibi da wannan al'amudi zuwa wurina don cutarwa ba.

53. Allah na Ibrahim da Nahor, Allah na mahaifinsu, ya shara'anta tsakaninmu.” Saboda haka Yakubu ya rantse da martabar mahaifinsa Ishaku.

54. Yakubu kuwa ya miƙa hadaya a bisa dutsen, ya kirawo iyalinsa su ci abinci, suka kuwa ci abinci suka zauna dukan dare a bisa dutsen.

55. Da sassafe, Laban ya tashi ya sumbaci jikokinsa, da 'ya'yansa mata, ya sa musu albarka. Sa'an nan ya tashi ya koma gida.

Karanta cikakken babi Far 31