Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 30:29-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Yakubu ya ce masa, “Kai da kanka ka san barantakar da na yi maka, yadda bisashenka suka yawaita a hannuna.

30. Gama kafin in zo, kana da 'yan kima ne, ga shi, sun ƙaru da yawa, Ubangiji kuwa ya sa maka albarka duk inda na juya. Amma yanzu, sai yaushe zan hidimta wa nawa gidan?”

31. Ya ce, “Me zan ba ka?”Yakubu ya ce, “Ba za ka ba ni kome ba, in da za ka yi mini wannan, sai in sāke kiwon garkenka in lura da shi,

32. bar ni, in ratsa garkenka duka yau, in keɓe dukan masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki, waɗannan ne za su zama ladana.

33. Ta haka amincina zai shaide ni a gabanka a sa'ad da ka zo bincike hakkina. Duk wanda aka iske ba dabbare-dabbare ba ne, kuma ba babare-babare ba ne cikin awaki, ba kuma baƙi ba ne a cikin raguna, in aka samu a wurina, sai a ɗauka, na sata ne.”

34. Laban ya ce, “Madalla! Bari ya kasance kamar yadda ka faɗa.”

35. Amma a ran nan Laban ya ware bunsuran da suke dabbare-dabbare da masu sofane, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare da kyalloli, da dukan baƙaƙen tumaki, ya danƙa su a hannun 'ya'yansa maza,

36. ya sa nisan tafiya ta kwana uku tsakaninsu da Yakubu, Yakubu kuma ya ci gaba da kiwon sauran garken Laban.

37. Yakubu ya samo ɗanyun tsabgogin aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bayyanar da fararen zane-zanensu a fili.

38. Ya kafa tsabgogin da ya ɓare a gaban garkuna a magudana, wato kwamame na banruwa, don sukan yi barbara a wurin sa'ad da suka zo shan ruwa.

39. Garkunan suka yi barbara a gaban tsabgogin, don haka garkunan sukan haifi masu zāne, dabbare-dabbare da masu sofane.

40. Yakubu kuwa ya keɓe 'yan raguna, ya sa garkuna su fuskanci tsabgogin da ya shasshauta, da dukan baƙaƙen da suke cikin garken Laban. Sai ya ware waɗanda suke nasa, bai kuwa haɗa su da garken Laban ba.

41. A kowane lokacin da ƙarfafan yake barbara Yakubu yakan sa tsabgogin a magudana a gaban idanun garken, domin su yi barbara a tsakanin tsabgogin.

42. Amma ga marasa ƙarfi na garken, ba ya sa musu. Don haka marasa ƙarfin ne na Laban, ƙarfafan kuwa na Yakubu.

Karanta cikakken babi Far 30