Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 30:10-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Kuyangar Lai'atu, Zilfa, ta haifa wa Yakubu ɗa.

11. Lai'atu kuma ta ce, “Sa'a!” Saboda haka ta sa masa suna Gad.

12. Kuyangar Lai'atu ta sāke haifa wa Yakubu ɗa na biyu.

13. Lai'atu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Gama mata za su ce da ni mai farin ciki,” saboda haka ta raɗa masa suna Ashiru.

14. A kwanakin kakar alkama, Ra'ubainu ya fita ya samo manta uwa a saura, ya kawo wa mahaifiyarsa Lai'atu. Sai Rahila ta ce wa Lai'atu, “Ina roƙonki, ɗiba mini daga cikin manta uwar da ɗanki ya samo.”

15. Amma ta ce mata, “Kanƙanen abu ne da kika ƙwace mini mijina? Za ki kuma ƙwace manta uwar da ɗana ya samo kuma?”Rahila ta ce, “To, in haka ne, bari ya kwana tare da ke a daren yau a maimakon manta uwar da ɗanki ya samo.”

16. Sa'ad da Yakubu ya komo daga saura da maraice, Lai'atu ta fita ta tarye shi, ta ce, “Sai ka shigo wurina, gama na riga na ijarar da kai da manta uwar da ɗana ya samo.” Saboda haka ya kwana tare da ita a daren nan.

17. Allah ya saurari Lai'atu, ta kuwa yi ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na biyar.

18. Lai'atu ta ce, “Allah ya yi mini sakamako domin na ba da kuyangata ga mijina,” saboda haka ta raɗa masa suna Issaka.

19. Lai'atu ta sāke yin ciki ta kuwa haifa wa Yakubu ɗa na shida.

Karanta cikakken babi Far 30