Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 2:5-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. a sa'an nan ba tsire-tsiren saura a duniya, ƙananan ganyayen saura kuma ba su riga sun tsiro ba, gama Ubangiji Allah bai sa a yi ruwa bisa duniya ba tukuna. A lokacin kuwa babu wani wanda zai noma ƙasar,

6. amma sai ƙāsashi yake tasowa daga ƙasa ya shayar da fuskar ƙasa duka.

7. Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.

8. Ubangiji Allah kuwa ya dasa gona a Aidan, wajen gabas, a can ya sa mutumin da ya siffata.

9. Ubangiji Allah ya sa kowane itace mai kyan gani, mai amfani domin abinci, ya tsiro, itacen rai kuwa yana tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta.(Far 3.22,24; W. Yah 2.7; 22.2,14,19; Eze 47.12

10. Wani kogi kuma ya malalo daga Aidan ya shayar da gonar, daga nan kuwa ya rarrabu ya zama kogi huɗu.

11. Sunan na fari Fishon, shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya.

12. Zinariyar ƙasan nan kuwa kyakkyawa ce. Akwai kuma duwatsu masu daraja a wurin.

13. Sunan kogi na biyu Gihon, shi ne wanda yake malala kewaye da ƙasar Kush.

14. Sunan kogi na uku Taigiris ne, wanda yake malala gabashin Assuriya. Kogi na huɗu kuwa Yufiretis ne.

Karanta cikakken babi Far 2