Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 1:14-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Allah kuwa ya ce, “Bari haskoki su kasance a cikin sararin, su raba tsakanin yini da dare, su kuma zama alamu, da yanayi na shekara, da wokatai.

15. Bari kuma su zama haskoki a cikin sarari su haskaka duniya.” Haka nan kuwa ya kasance.

16. Allah kuwa ya yi manyan haskokin nan biyu, haske mafi girma ya mallaki yini, ƙaramin kuwa ya mallaki dare, ya kuma yi taurarin.

17. Allah ya sa su a cikin sarari su haskaka duniya,

18. su yi mulkin yini da kuma dare, su raba tsakanin haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

19. Ga maraice, ga safiya, kwana na huɗu ke nan.

20. Allah kuwa ya ce, “Bari ruwaye su fid da ɗumbun masu rai, bari tsuntsaye kuma su riƙa tashi bisa duniya ƙarƙashin sarari.”

21. Allah kuwa ya halicci manya manyan dodani na teku da kowane irin mai rai da yake motsi, waɗanda suke a cikin ruwaye, da kuma kowane irin tsuntsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

22. Sai Allah ya sa musu albarka, yana cewa, “Ku hayayyafa, ku kuma riɓaɓɓanya, ku cika ruwayen tekuna, tsuntsaye kuma ku hayayyafa cikin duniya.”

23. Ga maraice, ga safiya, kwana na biyar ke nan.

24. Allah kuwa ya ce, “Bari duniya ta fid da masu rai bisa ga irinsu, shanu, da abubuwa masu rarrafe, da dabbobin duniya bisa ga irinsu.”

25. Allah kuwa ya yi dabbobin gida bisa ga irinsu, da kuma na jeji, manya da ƙanana, da kowane irin mai rarrafe bisa ƙasa bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

Karanta cikakken babi Far 1