Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 9:4-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sa'an nan dukan waɗanda suka yi rawar jiki saboda maganar Allah na Isra'ila, saboda rashin aminci na waɗanda suka komo daga zaman talala, suka taru, suka kewaye ni sa'ad da nake zaune a ruɗe, har lokacin yin sadakar yamma.

5. A lokacin sadakar yamma ɗin, sai na tashi daga yin azumi, da rigata da alkyabbata yagaggu. Na rusuna a gwiwoyina, na ɗaga hannuwana zuwa ga Ubangiji Allahna.

6. Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.

7. Tun daga zamanin kakanninmu muna da babban laifi. Saboda zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu, aka bashe mu a hannun sarakunan waɗansu ƙasashe, aka bashe mu ga takobi, aka kai mu bauta, aka washe mu, aka kunyatar da mu kamar yadda yake a yau.

8. Amma a yanzu a wannan ɗan lokaci Ubangiji Allahnmu ya yi mana alheri da ya bar mana ringi, ya kuma ba mu wuri a wurinsa mai tsarki, inda za mu zauna lafiya domin Allahnmu ya waye mana ido, ya kuma ba mu 'yar wartsakewa daga bautarmu.

9. Gama mu bayi ne, duk da haka Allahnmu bai manta da mu a bautarmu ba, amma ya sa muka sami tagomashi a wurin sarakunan Farisa, suka iza mu domin mu gina Haikalin Allahnmu, mu sāke gyaransa, mu kuma gina garu a Yahuza da Urushalima.

10. “Yanzu, me za mu ce bayan wannan, ya Allahnmu, gama mun manta da umarnanka.

Karanta cikakken babi Ezra 9