Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 9:12-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Domin haka kada ku aurar musu da 'ya'yanku mata, kada kuma ku auro wa 'ya'yanku 'yan matansu, kada kuma ku nemi zaman arziki da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku ci albarkar ƙasar, har ku bar ta gādo ga 'ya'yanku har abada.’

13. Bayan wannan dukan abubuwan nan suka same mu saboda mugayen ayyukanmu da zunubanmu masu yawa. Ya Allahnmu, ga shi ma, ka hukunta mu kaɗan bisa ga yawan zunubanmu, ka kuma bar mana wannan ringi.

14. Za mu sake ƙetare umarninka, mu yi aurayya da mutanen da suke yin waɗannan ƙazanta? Ba za ka yi fushi da mu, ka ƙone mu da fushinka har babu ringi ba?

15. Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai mai adalci ne, gama ka bar mana ringin da ya tsira kamar yadda yake a yau. Ga mu nan gabanka da zunubinmu, gama ba wanda zai iya tsayawa a gabanka saboda wannan.”

Karanta cikakken babi Ezra 9