Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 3:2-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sai Yeshuwa ɗan Yehozadak tare da 'yan'uwansa, firistoci, da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel tare da 'yan'uwansu, suka tashi suka gina bagaden Allah na Isra'ila domin a miƙa hadayu na ƙonawa kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, mutumin Allah.

3. Suka ta da bagaden a wurinsa domin suna jin tsoron mutanen ƙasar. Suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa safe da yamma.

4. Suka kuma kiyaye Idin Bukkoki kamar yadda aka rubuta, suna miƙa hadayu na ƙonawa kowace rana bisa ga yawan adadin hadayun da ake bukata.

5. Daga baya kuma suka miƙa hadayun ƙonawa na yau da kullum, da hadayu na amaryar wata, da ƙayyadaddun hadayu na idodin Ubangiji, da hadayu na amaryar wata, da ƙayyadaddun Ubangiji.

6. Tun daga rana ta fari ga watan bakwai, suka fara miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa, amma ba a riga an aza harsashin Haikalin Ubangiji ba.

Karanta cikakken babi Ezra 3