Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 10:4-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai ka tashi, gama wannan hakkinka ne, mu kuwa muna tare da kai. Sai dai ka yi ƙarfin hali, ka yi shi.”

5. Ezra kuwa ya tashi, ya sa firistoci da suke shugabanni, da Lawiyawa, da dukan mutanen Isra'ila su rantse, cewa za su yi abin da aka ce. Sai suka yi rantsuwar.

6. Sa'an nan Ezra ya tashi daga Haikalin Allah, ya tafi gidan Yohenan ɗan Eliyashib, amma ko da ya tafi can bai ci abinci ba, bai kuma sha ruwa ba, gama yana baƙin ciki saboda rashin aminci na waɗanda suka dawo daga zaman talala.

7. Sai aka yi shela a dukan Yahuza da Urushalima, cewa dukan waɗanda suka komo daga zaman talala, su hallara a Urushalima.

8. Duk wanda bai zo a cikin kwana uku ba, za a washe shi, a kuma ware shi daga jama'ar da suka dawo daga zaman talala. Haka shugabanni da dattawa suka umarta.

9. Sai dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, suka hallara a Urushalima kafin kwana uku, a ran ashirin ga watan tara. Mutanen suka zauna a dandalin Haikali, suna rawar jiki saboda al'amarin, da kuma saboda babban ruwan sama.

10. Ezra firist kuwa ya miƙe tsaye ya ce wa jama'a, “Kun yi rashin aminci, kun auri mata baƙi, ta haka kuka ƙara zunubin Isra'ila.

11. Yanzu sai ku hurta wa Ubangiji Allah na kakanninku, laifinku, ku kuma aikata nufinsa. Ku ware kanku daga mutanen ƙasar da mata baƙi.”

12. Dukan taron jama'a suka amsa da babbar murya, suka ce, “Haka nan ne, haka nan ne, dole ne mu yi yadda ka faɗa.

13. Amma mutane suna da yawa, a lokacin kuwa ana marka, ba za mu iya tsayawa a fili ba, aikin nan kuma ba na kwana ɗaya, ko biyu ba ne, gama mun yi laifi sosai wajen wannan al'amari.

14. Bari shugabanninmu su wakilci dukan taron jama'a, bari kuma dukan waɗanda suke garuruwanmu da suka auri mata baƙi su zo a ƙayyadadden lokaci tare da dattawa da alƙalan garuruwansu, har lokacin da Allah ya huce daga fushinsa a kanmu saboda al'amarin nan.”

Karanta cikakken babi Ezra 10