Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 7:9-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ba zan yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan hukunta ku bisa ga ayyukanku sa'ad da kuke tsakiyar aikata ƙazantarku, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji wanda yake hukunta ku.

10. “Ga rana ta zo. Ƙaddararku ta zo, rashin gaskiya ta yi fure, girmankai kuma ya yi toho.

11. Hargitsi ya habaka, ya zama sandan mugunta. Ba wanda zai ragu cikinsu, ko yawaitarsu, ko dukiyarsu, ko wani muhimmi a cikinsu.

12. “Lokaci ya yi, ranar ta gabato, kada mai saye ya yi farin ciki, kada kuma mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama fushina yana kan taron jama'a duka.

13. Mai sayarwa ba zai ta da ciniki ba sa'ad da suke da rai, gama fushina yana bisa kan dukan taron jama'arsu, ba zai fasa ba. Ba wanda yake zamansa cikin zunubi da zai iya shiryar da kansa.”

14. “Sun busa ƙaho, sun gama shiri duka, amma ba wanda ya tafi yaƙi, gama fushina yana kan dukan taron jama'a.

15. Takobi yana zare a waje, annoba da yunwa suna ciki. Wanda yake waje takobi zai kashe shi, wanda kuma yake ciki annoba da yunwa za su kashe shi.

16. Idan akwai waɗanda suka tsere, za a same su a kan duwatsu kamar kurciyoyin kwaruruka, suna baƙin ciki dukansu, kowa yana baƙin ciki saboda laifinsa.

17. Dukan hannuwa sun raunana, dukan gwiyoyi kuma sun zama marasa ƙarfi kamar ruwa.

18. Sun sa tufafin makoki, razana ta kama su, fuskokinsu kuma suna cike da kunya, akwai sanƙo a kawunansu.

19. Sun watsar da azurfarsu a titi, zinariyarsu kuma ta zama kamar ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba, a ranar fushin Ubangiji. Ba za su iya ƙosar da su ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu.

20. Suna fariyar banza da kyawawan kayan adonsu, na zinariya da azurfa. Da su suka yi siffofi masu banƙyama, da ƙazantattun abubuwa. Domin haka zan maishe su ƙazantattun abubuwa a gare su.

21. “Zan ba da su ganima ga baƙi, da kwaso ga mugayen mutanen ƙasar. Za su lalatar da su.

22. Zan kuwa juya daga gare su. Zan bar su su ƙazantar da Haikalina. Mafasa za su shiga su ƙazantar da shi.

23. “Sai ka ƙera surƙa, gama ƙasar tana cike da alhakin jini, birnin kuma yana cike da hargitsi.

Karanta cikakken babi Ez 7