Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 7:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ya kai, ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce wa ƙasar Isra'ila, matuƙa ta yi a kan kusurwa huɗu na ƙasar!

3. “Yanzu matuƙarki ta yi. Zan fashe fushina a kanki, zan kuma shara'anta ki bisa ga ayyukanki, in hukunta ki saboda dukan ƙazantarki.

4. Ba zan yafe miki ba, ba kuwa zan ji tausayinki ba, amma zan hukunta ki saboda ayyukanki sa'ad da kike tsakiyar aikata ƙazantarki. Sa'an nan za ki sani ni ne Ubangiji.”

5. Ubangiji Allah ya ce, “Masifa a kan masifa, ga shi, tana zuwa!

6. Matuƙa ta yi, ta farka a kanki, ga shi, ta yi!

7. Ƙaddararku ta auko muku, ya ku mazaunan ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato, ranar tunzuri, ba ta murna da ta sowa a kan duwatsu ba.

8. “Yanzu, ba da jimawa ba, zan fashe hasalata a kanku, in aukar da fushina a kanku, in hukunta ku bisa ga ayyukanku. Zan hukunta ku saboda dukan ƙazantarku.

9. Ba zan yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan hukunta ku bisa ga ayyukanku sa'ad da kuke tsakiyar aikata ƙazantarku, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji wanda yake hukunta ku.

Karanta cikakken babi Ez 7