Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 6:11-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ubangiji Allah ya ce, “Ka tafa hannunka, ka ɗage ƙafarka, sa'an nan ka ce, ‘Kaito, kaito, saboda dukan mugayen abubuwan ƙyama da mutanen Isra'ila suka yi, gama takobi, da yunwa, da annoba za su kashe su.

12. Annoba za ta kashe wanda yake nesa, wanda yake kusa kuwa takobi zai kashe shi. Yunwa kuma za ta kashe wanda yaƙi ya kewaye shi. Ta haka zan aukar da fushina a kansu.

13. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, sa'ad da gawawwakinsu sun kwanta tare da gumakansu kewaye da bagadansu a kan kowane tudu, da kan tsaunuka, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, da ƙarƙashin itacen oak mai ganye, duk inda suka miƙa turare mai ƙanshi ga dukan gumakansu.

14. Zan nuna ikona a dukan ƙasar, in mai da ita da wuraren zamansu duka hamada. Ƙasarsu za ta zama hamada har zuwa Dibla. Kowa zai sani ni ne Ubangiji.”’

Karanta cikakken babi Ez 6