29. Ubangiji ya ce, “Wannan ita ce hanyar da za ku raba gādo tsakanin kabilan Isra'ila. Waɗannan kuwa su ne yankunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”
30. “Ƙofofin birnin a gefen arewa, kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500] ne.
31. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Ra'ubainu, da Ƙofar Yahuza, da Ƙofar Lawi. Ana kiran sunayen ƙofofin birnin da sunayen kabilan Isra'ila.
32. A gefen gabas, kamu dubu huɗu ne da ɗari biyar [4,500]. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Yusufu, da Ƙofar Biliyaminu, da Ƙofar Dan.
33. A gefen kudu, kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500]. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Saminu, da Ƙofar Issaka, da Ƙofar Zabaluna.
34. A gefen yamma, kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500] ne. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Gad, da Ƙofar Ashiru, da Ƙofar Naftali.
35. Da'irar birnin kamu dubu goma sha takwas [18,000] ne. Daga wannan lokaci za a kira birnin, ‘Ubangiji Yana Nan!”’