Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 48:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ga sunayen kabilan da rabon gādonsu. Yankin Dan, shi ne daga iyakar arewa daga tekun. Ya bi ta Hetlon zuwa ƙofar Hamat, har zuwa Hazar-enan wadda take iyakar Dimashƙu daga arewa, daura da Hamat. Ya zarce daga gabas zuwa yamma.

2. Yankin Ashiru yana kusa da yankin Dan, daga gabas zuwa yamma.

3. Yankin Naftali yana kusa da yankin Ashiru daga gabas zuwa yamma.

4. Yankin Manassa yana kusa da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma.

5. Yankin Ifraimu yana kusa da yankin Manassa daga gabas zuwa yamma.

6. Yankin Ra'ubainu yana kusa da yankin Ifraimu daga gabas zuwa yamma.

7. Yankin Yahuza yana kusa da yankin Ra'ubainu daga gabas zuwa yamma.

8. “Kusa da yankin Yahuza daga gabas zuwa yamma, sai yankin da za ku keɓe. Faɗinsa kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], tsawonsa kuma daidai da tsawon yankunan kabilai daga gabas zuwa yamma. Haikali zai kasance a tsakiyar yankin.

9. “Yankin da za ku keɓe wa Ubangiji, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗinsa kuwa kamu dubu goma [10,000].

10. Wannan tsattsarkan yanki shi ne rabon firistoci. Tsawonsa wajen arewa, kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] ne, faɗinsa a wajen yamma kuwa, kamu dubu goma [10,000] ne, a wajen gabas faɗinsa kamu dubu goma [10,000], a wajen kudu tsawonsa kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000]. Haikalin Ubangiji zai kasance a tsakiyarsa.

11. Wannan zai zama na keɓaɓɓun firistoci daga zuriyar Zadok waɗanda suka kiyaye umarnina, ba su karkace kamar yadda Lawiyawa suka yi lokacin da jama'ar Isra'ila suka karkace ba.

12. Zai zama rabonsu daga tsattsarkan yankin ƙasar da take kusa da yankin Lawiyawa.

13. Gab da yankin firistoci, Lawiyawa za su sami rabo mai tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗi kuma kamu dubu goma [10,000]. Tsawonsa duka zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗi kuwa kamu dubu goma [10,000].

14. Daga cikinsa ba za su sayar ba, ko su musayar, ba kuma za su jinginar da wannan keɓaɓɓen yankin ƙasa ba, gama tsattsarka ne na Ubangiji.

Karanta cikakken babi Ez 48