Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 47:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya komo da ni zuwa ƙofar Haikalin, sai ga ruwa yana bulbulowa daga ƙarƙashin bakin ƙofar Haikalin a wajen gabas, gama Haikalin na fuskantar gabas. Ruwan kuwa yana gangarowa daga gefen kudancin bakin ƙofar Haikalin, a kudancin bagaden.

2. Sai ya fito da ni ta hanyar ƙofar arewa, ya kewaya da ni zuwa ƙofar waje wadda take fuskantar gabas. Ruwan kuwa yana gangarowa kaɗan kaɗan daga wajen kudu.

3. Mutumin ya nufi wajen gabas da ma'auni a hannunsa, ya auna kamu dubu, sa'an nan ya sa ni in haye ruwan. Zurfin ruwan ya kama ni idon ƙafa.

4. Sai kuma ya auna kamu dubu, ya sa ni in haye ruwan. Zurfin ruwan kuwa ya kama ni gwiwa. Sai ya sāke auna kamu dubu, ya sa in haye ruwan, sai zurfin ruwan ya kai ga kama ni gindi.

5. Ya sāke auna kamu dubu kuma, sai ruwan ya zama kogi har ban iya in haye ba, gama ruwan ya hau, ya zama da zurfin da ya isa ninƙaya. Ya zama kogin da ba za a iya hayewa ba.

Karanta cikakken babi Ez 47