Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 45:3-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. A cikin yanki mai tsarki za ka auna tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], da faɗi kamu dubu goma [10,000], inda Wuri Mafi Tsarki zai kasance.

4. Wannan yanki shi ne zai zama wuri mai tsarki na ƙasar. Zai zama na firistoci waɗanda suke hidima a cikin Haikali, waɗanda suke kusatar Ubangiji don su yi masa hidima. Wurin zai zama wurin gina gidajensu da kuma wuri mai tsarki domin Haikalin.

5. Wani sashi kuma mai tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], da faɗi kamu dubu goma [10,000], zai zama na Lawiyawa masu hidima cikin Haikalin, zai zama wurin da za su mallaka, su zauna a ciki.

6. Za ku tsaga wa birnin hurumi mai fāɗi kamu dubu biyar, da tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], rabe da yankin nan mai tsarki. Hurumin zai zama na mutanen Isra'ila duka.”

7. “Ƙasar da take a sashin yankin nan mai tsarki, da hurumin birnin, zai zama na sarki. Zai zama hannun riga da yanki mai tsarki da hurumin birnin a wajen yamma da gabas. Tsawonta zai zama daidai da yanki ɗaya na yankunan kabilan. Za ta miƙe daga yamma zuwa iyakar ƙasar daga gabas.

8. Wannan zai zama yankin ƙasarsa a cikin Isra'ila. Sarakunana kuma ba za su ƙara zaluntar mutanena ba, amma za su ba mutanen Isra'ila ƙasar bisa ga kabilansu.”

9. “Ni Ubangiji Allah na ce ku sarakunan Isra'ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari'a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, ni Ubangiji Allah na faɗa.

10. “Sai ku kasance da ma'aunai na gaskiya, kamar su mudu da garwa.

11. “Kwanon awo na mudu da na garwa girmansu ɗaya ne. Garwa goma ganga guda ne. Ganga ita ce za ta zama fitaccen ma'auni.

12. “Shekel zai zama gera ashirin. Mainanku ɗaya zai zama shekel sittin.”

13. “Wannan ita ce bayarwar da za ku yi. Za ku ba da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta alkama, da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta sha'ir.

14. Za ku ba da ɗaya daga cikin goma ta garwa daga kowace ganga ta mai. Ganga tana cin garwa goma.

15. Za ku ba da tunkiya ɗaya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu, a cikin Isra'ila.“Waɗannan su ne hadayu na gari, da na ƙonawa, da na salama, domin a yi musu kafara, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16. “Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwar domin Sarkin Isra'ila.

17. Sarki ne da nawayar ba da hadayun ƙonawa, da na gari, da na sha a lokacin idodi da na amaryar wata, da ranakun Asabar, da lokacin dukan ƙayyadaddun idodin mutanen Isra'ila. Zai kuma ba da hadayu don zunubi da na salama domin a yi wa mutanen Isra'ila kafara.”

18. “Ni Ubangiji Allah na ce, rana ta fari ga watan fari, za ku ɗauki bijimi marar lahani don a tsarkake Haikalin.

19. Firist zai ɗibi jinin hadaya domin zunubi ya shafa shi a madogaran ƙofar Haikalin, da kusurwa huɗu na dakalin bagaden, da ginshiƙan ƙofar fili na can ciki.

Karanta cikakken babi Ez 45