Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 40:41-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

41. A gab da ƙofar akwai tebur huɗu, a waje ɗaya kuma akwai huɗu. Duka guda takwas ke nan, inda za a riƙa yanka dabbobin da za a yi hadaya da su.

42. Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu, tsawon da faɗin kowanne kamu ɗaya da rabi rabi ne, tsayi kuwa kamu guda ne. A nan za a ajiye kayan yanka hadayar ƙonawa, da ta sadaka.

43. Aka kakkafa ƙugiyoyi kewaye da cikin ɗakin, tsawonsu taƙi-taƙi. Za a riƙa ajiye naman hadaya a kan teburorin.

44. Ya kai ni fili na can ciki, sai ga ɗakuna biyu a filin. Ɗaya yana wajen ƙofar arewa, yana fuskantar kudu. Ɗayan kuma yana wajen ƙofar kudu yana fuskantar arewa.

45. Sai ya ce mini, “Wannan ɗaki wanda yake fuskantar kudu na firistoci ne waɗanda suke lura da Haikalin.

46. Ɗakin da yake fuskantar arewa na firistoci ne waɗanda suke lura da bagade. Waɗannan su ne zuriyar Zadok waɗanda su kaɗai ne daga cikin Lawiyawa da suke da iznin kusatar Ubangiji don su yi masa hidima.”

47. Ya auna filin, tsawonsa kamu ɗari ne, faɗinsa kuma kamu ɗari, wato murabba'i ke nan. Bagade kuma yana a gaban Haikalin.

48. Ya kuma kai ni a shirayin Haikalin. Ya auna ginshiƙan shirayin, kamu biyar ne a kowane gefe. Faɗin ƙofar kuwa kamu uku ne a kowane gefe.

49. Tsawon shirayin kamu ashirin ne, faɗinsa kuwa kamu goma sha ɗaya. Akwai matakan hawa, akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe.

Karanta cikakken babi Ez 40