Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 40:25-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Akwai tagogi kewaye da ƙofar, da shirayinta kamar na sauran. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuwa kamu ashirin da biyar.

26. Tana da matakai bakwai. Shirayinta yana daga can ciki. An zana siffar itatuwan dabino a ginshiƙanta, ɗaya a kowane gefe.

27. Akwai wata ƙofa a kudancin fili na can ciki. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofa kamu ɗari.

28. Ya kuma kai ni fili na can ciki, wajen ƙofar kudu, sai ya auna ƙofar, girmanta daidai yake da na sauran.

29. Haka kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta, girmansu ɗaya yake da na sauran. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kamu ashirin da biyar ni.

30. Akwai shirayi kewaye, tsawonsa kamu ashirin da biyar ne, faɗinsa kuma kamu biyar ne.

31. Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje. An zana siffar itatuwan dabino a ginshikanta. Tana kuma da matakai takwas.

32. Sai kuma ya kai ni a fili na can ciki wajen gabas. Ya auna ƙofar, girmanta daidai yake da na sauran.

33. Haka nan kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta, girmansu daidai yake da na sauran. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuma kamu ashirin da biyar.

34. Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje. Aka zana siffar itatuwan dabino a kan ginshiƙanta a kowane gefe. Tana da matakai takwas.

35. Sa'an nan kuma ya kai ni ƙofar arewa, ya auna ta. Girmanta daidai yake da na sauran.

36. Haka kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuma kamu ashirin da biyar.

Karanta cikakken babi Ez 40