Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 39:18-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Za su ci naman mutane masu iko, su sha jinin shugabannin duniya, waɗanda aka kashe kamar yadda ake yanka raguna, da 'yan tumaki, da awaki, da bijimai, da dukan turkakkun Bashan.

19. Za su ci kitse, har su gundura, su sha jini kuma, har su bugu a idin da nake shirya musu.

20. Za a ƙosar da su da naman dawakai, da na mahayansu da na mutane masu iko, da na dukan mayaƙa, ni Ubangiji na faɗa.”

21. “Zan nuna ɗaukakata a cikin al'ummai, dukan al'ummai kuwa za su ga hukuncin da na yi da ikon da na nuna kansu.

22. Tun daga wannan rana har zuwa gaba, jama'ar Isra'ila za su sani, ni ne Ubangiji Allahnsu.

23. Al'ummai kuma za su sani an kai jama'ar Isra'ila zaman bautar talala saboda muguntarsu, domin sun yi mini ha'inci, ni kuwa na kawar da fuskata daga gare su, na bashe su a hannun abokan gābansu, suka ci su da yaƙi.

24. Na yi gwargwadon lalatarsu da laifofinsu, na kawar da fuskata daga gare su.

25. “Saboda haka, ni Ubangiji Allah, na ce yanzu zan komo da zuriyar Yakubu daga bauta in nuna mata jinƙai. Zan yi kishi domin sunana mai tsarki.

26. Sa'ad da suka komo suka zauna lafiya a ƙasarsu, za su manta da abin kunyar da suka yi da dukan ha'incin da suka yi mini. Ba wanda zai ƙara firgita su, ba kuwa mai tsorata su.

27. Zan nuna wa sauran al'umma ni mai tsarki ne ta wurin komo da mutanen Isra'ila daga cikin al'ummai, da ƙasashen al'ummai magabtansu.

28. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu, domin na kore su daga ƙasarsu zuwa bautar talala cikin al'ummai, sa'an nan na sāke tattaro su zuwa cikin ƙasarsu. Daga cikinsu ba zan bar ko ɗaya a cikin al'ummai ba.

29. Ba kuma zan ƙara kawar da fuskata daga gare su ba, sa'ad da na saukar da Ruhuna a kan jama'ar Isra'ila, ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 39