Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 39:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa Gog shugaban Rosh, da Meshek, da Tubal cewa, ‘Ni Ubangiji Allah ina gāba da kai.

2. Zan juya ka in sa ka gaba in tashi daga ƙurewar arewa, in kawo ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra'ila.

3. Sa'an nan zan karya bakan da yake a hannun hagunka, in sa kiban da suke a hannun damanka su fāɗi.

4. Za ka fāɗi matacce a kan duwatsun Isra'ila, kai da dukan rundunanka, da jama'ar da suke tare da kai. Zan ba da gawawwakinka ga tsuntsaye da dabbobi masu cin nama.

5. Za ka mutu a filin saura, gama haka ni Ubangiji Allah na faɗa.’

6. Zan aika da wuta a kan Magog, da a kan waɗanda suke zaman lafiya a ƙasashen gāɓar teku, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.

7. Zan sanar da sunana mai tsarki a tsakiyar jama'ata, wato Isra'ila, ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, al'ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji Mai Tsarki a cikin Isra'ila.

8. “Ga shi, ranar da na ambata tana zuwa, hakika kuwa tana zuwa, ni Ubangiji Allah na faɗa.

Karanta cikakken babi Ez 39