Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 38:16-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Za ka zo ka yi yaƙi da mutanen Isra'ila, za ka rufe su kamar yadda girgije yakan rufe sararin sama. A kwanaki na ƙarshe zan kawo ka ka yi yaƙi da ƙasata domin al'ummai su san ni sa'ad da na bayyana tsarkina a gabansu ta wurin abin da ka yi.”’

17. Ubangiji Allah ya ce, “Kai ne wanda na yi magana a kanka a zamanin dā ta wurin bayina annabawan Isra'ila, cewa a shekaru masu zuwa zan kawo ka, ka yaƙe su.

18. Amma a wannan rana sa'ad da Gog zai kawo wa ƙasar Isra'ila yaƙi, ni Ubangiji Allah zan hasala.

19. Gama a kishina da zafin hasalata na hurta, cewa a wannan rana za a yi babbar girgiza a ƙasar Isra'ila.

20. Kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da bisashe, da dukan masu rarrafe, da dukan mutanen da suke duniya, za su yi makyarkyata a gabana. Za a jefar da duwatsu ƙasa, tsaunuka za su fādi, kowane bango zai rushe.

21. Zan razana Gog da kowace irin razana, ni Ubangiji Allah na faɗa. Mutanensa za su sassare junansu da takubansu.

22. Zan hukunta shi da annoba da kuma zub da jini. Zan yi masa ruwa da ƙanƙara, da wuta, da kibritu za a makaka a kansa da rundunarsa, da dukan jama'ar da suke tare da shi.

23. Da haka kuwa zan bayyana girmana da tsarkina in kuma sanar da kaina ga al'ummai. Ta haka za su sani ni ne Ubangiji.”

Karanta cikakken babi Ez 38