Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 32:29-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. “Edom kuma tana can tare da sarakunanta da dukan shugabanninta masu iko, Suna kwance tare da waɗanda aka kashe da takobi, marasa imani, masu gangarawa zuwa cikin kabari.

30. “Dukan shugabannin arewa suna can, da dukan Sidoniyawa. Da kunya, suna gangarawa tare da waɗanda aka kashe, ko da yake a dā sun haddasa tsoro saboda ikonsu. Yanzu suna kwance tare da marasa imani waɗanda aka kashe da takobi. Suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa cikin kabari.

31. “Sa'ad da Fir'auna zai gan su, zai ta'azantu a kan rundunarsa da aka kashe da takobi. Lalle Fir'auna da dukan rundunarsa za su ta'azantu. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

32. “Ko da yake na sa Fir'auna ya haddasa tsoro a duniya, duk da haka zan sa a kashe shi tare da rundunarsa. Za su kwanta tare da marasa imani waɗanda aka kashe da takobi. Ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 32