Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 32:20-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. “An zare takobi don a kashe jama'ar Masar. Za su fāɗi a tsakiyar waɗanda aka kashe da takobi.

21. Manyan jarumawa daga lahira za su yi magana a kansu da mataimakansu, su ce, ‘Marasa imani waɗanda aka kashe da takobi, sun gangaro, ga su nan kwance shiru!’

22. “Assuriya tana can da dukan taron jama'arta. Kaburburansu suna kewaye da ita. An kashe dukansu da takobi.

23. An binne su a can ƙurewar lahira. Taron jama'arta suna kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Su ne suka haddasa tsoro a cikin ƙasar.

24. “Elam tana can da dukan jama'arta kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Sun gangara da rashin imaninsu zuwa lahira. Su ne suka haddasa tsoro a duniya. Sun sha kunyarsu tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari.

25. An shirya mata gado tare da matattu. Kaburburan dukan sojojinta suna kewaye. Dukansu marasa imani ne, waɗanda aka kashe da takobi, amma a dā sun yaɗa tsoro a duniya. Yanzu kuwa suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari. An tara su tare da waɗanda aka kashe.

26. “Meshek da Tubal suna can da dukan sojojinsu. Kaburburan sojojinsu suna kewaye. Dukansu marasa imani ne, waɗanda aka kashe da takobi, gama sun yaɗa tsoro a duniya.

27. Ba su kwanta kusa da manyan jarumawan da aka kashe ba, waɗanda suka tafi lahira da makamansu, aka yi musu matasan kai da takubansu, aka rufe ƙasusuwansu da garkuwoyinsu, gama manyan jarumawan nan sun baza tsoro a duniya.

28. Amma za a karya ku, ku kwanta tare da marasa imani, tare da waɗanda aka kashe da takobi.

29. “Edom kuma tana can tare da sarakunanta da dukan shugabanninta masu iko, Suna kwance tare da waɗanda aka kashe da takobi, marasa imani, masu gangarawa zuwa cikin kabari.

30. “Dukan shugabannin arewa suna can, da dukan Sidoniyawa. Da kunya, suna gangarawa tare da waɗanda aka kashe, ko da yake a dā sun haddasa tsoro saboda ikonsu. Yanzu suna kwance tare da marasa imani waɗanda aka kashe da takobi. Suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa cikin kabari.

Karanta cikakken babi Ez 32