Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 29:5-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Zan yashe ka, kai da dukan kifayen kogunanka cikin jeji.Za ka fāɗi a fili, ba kuwa wanda zai ɗauke ka, ya binne ka.Zan sa ka zama abincin namomin jeji da tsuntsayen sararin sama.

6. A sa'an nan mazaunan Masar za su sani ni ne Ubangiji,Domin sun zama wa mutanenIsra'ila kamar sandan iwa.

7. Sa'ad da suka riƙe ka,Sai ka karye ka tsattsaga hannuwansu.Sa'ad da suka jingina da kai,Sai ka karye, har ka sa kwankwasonsu ya firgiza.

8. Saboda haka, ni Ubangiji Allah na ce zan jawo takobi a kanka, in kashe mutanenka, duk da dabbobi.

9. Ƙasar Masar za ta zama kufai, marar amfani. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.“ ‘Domin ka ce, “Kogin Nilu nawa ne, ni na yi shi,”

10. ina gāba da kai da kogunanka. Zan mai da ƙasar Masar kufai sosai, marar amfani, tun daga Migdol zuwa Sewene har zuwa iyakar Habasha.

11. Mutum ko dabba ba zai ratsa ta cikinta ba. Za ta zama kufai har shekara arba'in.

12. Zan mai da ƙasar Masar kufai fiye da sauran ƙasashe. Biranenta za su zama kufai marar amfani, fiye da sauran birane har shekara arba'in. Zan kuma warwatsar da Masarawa a cikin sauran al'umma.’ ”

13. Ubangiji Allah ya ce, “Bayan shekara arba'in zan tattaro Masarawa daga cikin sauran al'umma inda aka warwatsar da su.

Karanta cikakken babi Ez 29