Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 28:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,

2. “Dan mutum, ka faɗa wa Sarkin Taya, cewa Ubangiji Allah ya ce,‘Da yake zuciyarka ta cika da alfarma,Har ka ce kai allah ne,Kana zaune a mazaunin allah, kana zaune a tsakiyar tekuna,To, kai mutum ne kawai, ba allah ba,Ko da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah.

3. Lalle ka fi Daniyel hikima,Ba asirin da yake ɓoye a gare ka.

4. Ta wurin hikimarka da ganewarka ka samo wa kanka dukiya,Ka tattara zinariya da azurfa a baitulmalinka.

5. Saboda yawan hikimarka na yin kasuwanci, ka ƙara dukiyarka,Sai dukiyarka ta sa zuciyarka ta cika da alfarma.’

6. “Saboda haka Ubangiji Allah ya ce,‘Da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah,

7. Don haka zan tura baƙi a kanka,Waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al'umma.Za su zare takubansu a kan kyakkyawar hikimarka,Za su ɓara darajarka.

8. Za su jefar da kai cikin rami,Za ka mutu kamar waɗanda suka mutu a tsakiyar teku.

9. Har yanzu za ka ce kai allah ne a gaban waɗanda suke ji maka rauni, Ko da yake kai mutum ne kawai, ba Allah ba?

10. Za ka yi mutuwa irin ta kare ta hannun baƙi,Gama ni Ubangiji Allah na faɗa.’ ”

11. Ubangiji kuma ya yi magana da ni ya ce,

12. “Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Sarkin Taya, ka ce Ubangiji Allah ya ce,‘Kai cikakke ne, cike da hikima da jamali!

13. Kana cikin Aidan, gonar Allah.An yi maka sutura da kowane irin dutse mai daraja,Tare da zinariya.Kana da molo da abin busa.A ranar da aka halicce kaSuna nan cikakku.

14. Na keɓe ka ka zama mala'ika mai tsaro,Kana bisa tsattsarkan dutsen Allah,Ka yi tafiya a tsakiyar duwatsu na wuta.

15. Daga ranar da aka halicce ka ba ka da laifi cikin al'amuranka,Sai ran da aka iske mugunta a cikinka.

Karanta cikakken babi Ez 28