Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 24:21-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. in faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa Ubangiji Allah ya ce, ‘Zan ƙazantar da Haikalina, abin fariyarku, da abin da idanunku suke jin daɗin ganinsa, da abin faranta zuciyarku. 'Ya'yanku maza waɗanda kuka bari a baya, za a kashe su da takobi.

22. Za ku kuwa yi kamar yadda na yi, wato ba za ku ja amawali ba, ba kuwa za ku ci abincin masu makoki ba.

23. Za ku naɗa rawunanku, ku sa takalmanku, ba za ku kuma yi makoki ko kuka ba, amma za ku lalace cikin zunubanku. Za ku yi ta nishi.

24. Da haka Ezekiyel zai zama muku alama. Za ku yi kamar yadda ya yi duka. Sa'ad da wannan ya faru, za ku sani nine Ubangiji Allah.’

25. “Kai ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu madogararsu, da murnarsu, da darajarsu, da abin da idanunsu suka ji daɗin gani, da abin da yake faranta zuciyarsu, da 'ya'yansu mata da maza,

26. a wannan rana wanda ya tsere zai kawo maka labarin.

27. A ranar bakinka zai buɗe, za ka yi magana da wanda ya tsere, ba kuma za ka zama bebe ba. Da haka za ka zama alama gare su, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”

Karanta cikakken babi Ez 24