Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 23:17-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Sai Babilawa suka zo wurinta, a gadonta na nishaɗi, suka ƙazantar da ita ta wurin kwana da ita. Bayan da sun ƙazantar da ita, sai ta ji ƙyamarsu, ta rabu da su.

18. Ta yi ta karuwancinta a fili, ta bayyana tsiraicinta. Sai na ji ƙyamarta, na rabu da ita kamar yadda na rabu da 'yar'uwarta.

19. Duk da haka ta yi ta ƙara karuwancinta, tana tunawa da kwanakin 'yan matancinta, a lokacin da ta yi karuwancinta a ƙasar Masar.

20. Ta yi ta kai da kawowa tsakanin kwartayenta waɗanda al'auransu kamar na jakai ne, maniyyinsu kuwa kamar na dawakai ne.

21. Haka kika yi ƙawar zucin lalatar da kika yi a lokacin 'yan matancinki, sa'ad da Masarawa suka rungumi mamanki na ƙuruciya.”

22. “Domin haka, ya Oholiba, ni, Ubangiji Allah na ce zan kuta kwartayenki su yi gāba da ke, waɗanda kika ji ƙyamarsu, kika rabu da su. Daga kowane sashi zan sa su zo su yi gāba da ke.

23. Babilawa da dukan Kaldiyawa, da Fekod, da Showa, da Kowa, da dukan Assuriyawa tare da su, wato samari masu bansha'awa. Dukansu masu mulki ne, da shugabanni, da jarumawa, da shahararru, dukansu suna kan dawakai.

24. Za su zo daga arewa su yi yaƙi da ke da karusai, da kekunan dawakai, da rundunar mutane. Za su kafa miki sansani a kowace sashi su yi yaƙi da ke da sulke, da garkuwa, da kwalkwali. Zan danƙa shari'a a hannunsu, za su kuwa shara'anta ki da irin shari'arsu.

Karanta cikakken babi Ez 23