Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 22:24-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. “Ɗan mutum, ka ce mata, ‘Ke ƙasa ce marar tsarki, wadda ba a yi ruwan sama a kanki ba a lokacin da na yi fushi.’

25. Annabawanta suna kama da zakoki masu ruri waɗanda suke yayyage ganimar da suka samu. Sun kashe mutane, sun ƙwace dukiya da abubuwa masu daraja. Sun sa mata da yawa sun rasa mazansu.

26. Firistocinta sun karya dokokina, sun ƙazantar da tsarkakan abubuwana. Ba su bambanta tsakanin abin da yake mai tsarki da marar tsarki ba, ba su kuma koyar da bambancin da yake tsakanin halal da haram ba. Ba su kiyaye ranar Asabar ɗina ba, da haka suke saɓon sunana.

27. Shugabanninta sun zama kamar kyarketai masu yayyage ganima. Suna yin kisankai don su sami ƙazamar riba.

28. Annabawanta sun yi musu shafe da farar ƙasa, wato wahayan da suke gani, da duban da suke yi musu ƙarya ne. Suna cewa Ubangiji ne ya faɗa, alhali kuwa ni Ubangiji ban faɗa musu kome ba.

29. Mutanen ƙasar sun yi zalunci, sun yi fashi, sun zalunci matalauta da masu fatara. Ba su yi wa baƙo adalci ba, sai cuta.

30. Sai na nemi mutum a cikinsu wanda zai gina garun ya tsaya a hauren garun a gabana, domin kada in hallaka ƙasar, amma ban sami kowa ba.

31. Saboda haka na kwarara musu fushina, na ƙone su da wutar hasalata, na ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 22