Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 21:3-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ka faɗa wa ƙasar Isra'ila, ka ce, ni Ubangiji na ce ina gāba da ita. Zan zare takobina daga cikin kubensa, in karkashe adalai da mugaye daga cikinta.

4. Da yake zan karkashe adalai da mugaye daga cikinta, domin haka takobina zai fito daga cikin kubensa, ya karkashe dukan mutane daga Negeb wajen kudu, har zuwa arewa.

5. Dukan mutane kuwa za su sani, ni Ubangiji, na zare takobina daga cikin kubensa, ba kuwa zan sāke mayar da shi a kubensa ba.

6. “Domin haka, ya kai ɗan mutum, sai ka yi nishi, da ajiyar zuciya, da baƙin ciki mai zafi a gabansu.

7. Idan sun tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Saboda labarin abin da yake zuwa. Sa'ad da ya zo, kowace zuciya za ta narke, hannuwa duka za su yi suwu, kowane ruhu kuma zai suma, gwiwoyi duka kuwa za su rasa ƙarfi kamar ruwa. Ga shi, abin yana zuwa, zai tabbata,’ ni Ubangiji Allah na faɗa.”

8. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

9. “Ya ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce ni Ubangiji na ce,‘Takobi, takobi wasasshe,Kuma gogagge!

10. An wasa shi domin kisa,An goge shi don ya yi walwal kamar walƙiya!’Ba wanda zai iya tsai da shi, domin kun ƙi karɓar shawara.

11. An ba da takobin a goge shi domin a riƙe. An wasa shi, an kuma goge shi domin a ba mai kashewa.

12. Ka yi kuka, ka yi ihu, ya ɗan mutum, gama takobin yana gāba da jama'ata da dukan shugabannin Isra'ila. An ba da shugabanni da jama'ata ga takobi, sai ka buga ƙirjinka da baƙin ciki.

13. Gama ba don jarraba shi ba ne, sai me kuma idan ka raina sandan? Ni Ubangiji na faɗa.

14. “Domin haka, ya kai ɗan mutum, ka yi annabci, ka tafa hannuwanka, ka kaɗa takobi sau biyu, har sau uku. Takobin zai kashe waɗanda za a kashe. Takobi ne na yin kashe-kashe mai yawa. Zai kewaye su.

15. Zai sa zukatansu su narke, da yawa kuma su fāɗi a ƙofofinsu. Na ba da takobi mai walƙiya. An yi shi kamar walƙiya, an wasa shi don kashe-kashe.

16. Ka yi sara dama da hagu, duk inda ka juya.

17. Ni kuma zan tafa hannuwana, zan aukar da fushina, ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 21