Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 21:15-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Zai sa zukatansu su narke, da yawa kuma su fāɗi a ƙofofinsu. Na ba da takobi mai walƙiya. An yi shi kamar walƙiya, an wasa shi don kashe-kashe.

16. Ka yi sara dama da hagu, duk inda ka juya.

17. Ni kuma zan tafa hannuwana, zan aukar da fushina, ni Ubangiji na faɗa.”

18. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

19. “Ya ɗan mutum, ka nuna hanya biyu inda takobin Sarkin Babila zai bi. Dukansu biyu za su fito daga ƙasa ɗaya. Ka kafa shaidar hanya a kan magamin hanya zuwa birni.

20. Ka nuna wa takobin hanya zuwa Rabba ta Ammonawa, da hanya zuwa Yahuza, da Urushalima, birni mai garu.

21. Gama Sarkin Babila yana tsaye a mararrabar hanya, inda hanyar ta rabu biyu, yana yin dūbā, yana girgiza kibau, yana neman shawara wurin kan gida, yana dūbān hanta.

22. A hannun damansa, dūbā yana nuna abin da zai sami Urushalima. Zai kafa mata dundurusai, a yi kururuwar yaƙi, a rurrushe ƙofofinta da dundurusai, a gina mahaurai, a kuma gina hasumiyar yaƙi.

23. Amma a gare su dūbān nan ba gaskiya ba ce, gama sun riga sun yi rantsuwa mai nauyi, amma zai tuna musu da laifinsu, don a kama su.

24. Domin haka ni Ubangiji Allah na ce, tun da yake kun sa a tuna da laifofinku, an kuma tone su, laifofinku kuma sun bayyana cikin ayyukanku, kun tonu, to, za a kama ku a cikinsu.

25. “Kai kuma ƙazantaccen mugu, yariman Isra'ila, ranarka ta zo, lokacin hukuncinka ya yi.

26. Ni Ubangiji Allah na ce, ka cire rawaninka, ka ɗauke kambinka. Abubuwa ba za su kasance kamar yadda suke a dā ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da maigirma.

27. Halaka, halaka, zan hallakar, ba za a bar ko alama ba, sai mai shi ya zo, shi ne zan ba shi.”

28. “Kai ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce, ga abin da Ubangiji Allah ya ce a kan Ammonawa, da a kan zarginsu.‘An zare takobi don kashe-kashe,An goge shi don ya yi sheƙi kamar walƙiya!

29. Ka faɗa wa Ammonawa, cewa wahayin da suke gani ƙarya ne annabcin da suke yi kuma ƙarya ne. Su mugaye ne, ranar hukuncinsu tana zuwa. Za a sare wuyansu da takobi.

30. “‘Ka mai da takobinka cikin kubensa. Zan hukunta ka a ƙasarka inda aka haife ka.

31. Zan zubo maka da fushina, in hura maka wutar fushina. Zan bashe ka a hannun mugaye, gwanayen hallakarwa.

32. Za ka zama itacen wuta, za a zubar da jininka a tsakiyar ƙasar. Ba za a ƙara tunawa da kai ba, ni Ubangiji na faɗa.”’

Karanta cikakken babi Ez 21