Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 18:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. bai yi irin waɗannan abubuwa ba,] wato yana cin abinci a ɗakin tsafi, yana kwana da matar maƙwabcinsa,

12. yana kuma cin zalin matalauta masu fatara, yana yin ƙwace, ba ya mayar da abin da aka jinginar masa, yana bauta wa gumaka, yana kuma aikata abubuwa masu banƙyama,

13. yana ba da bashi da ruwa da ƙari, wannan ba zai rayu ba, gama ya aikata dukan abubuwan nan masu banƙyama. Zai mutu lalle, alhakin jininsa kuwa yana a kansa.

14. “Amma idan wannan mutum ya haifi ɗa wanda ya ga dukan laifofin da mahaifinsa ya yi, sa'an nan ya ji tsoro, bai kuwa yi haka ba,

15. bai ci abinci a ɗakin tsafi ba, bai bauta wa gumakan mutanen gidan Isra'ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba,

16. bai ci zalin kowa ba, bai karɓi jingina ba, bai yi ƙwace ba, amma yana ba mayunwaci abinci, yana ba huntu tufa,

17. yana hana hannunsa aikata mugunta, bai ba da bashi da ruwa ko wani ƙari ba, yana kiyaye ka'idodina, yana kuma bin dokokina, ba zai mutu saboda laifin mahaifinsa ba, amma zai rayu.

18. Amma mahaifinsa, da yake ya yi zalunci, ya yi wa ɗan'uwansa ƙwace ya aikata mugun abu a cikin mutanensa, zai mutu saboda muguntarsa.

19. “Za ku yi tambaya cewa, ‘Me ya sa ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba?’ Sa'ad da ɗan ya bi shari'a, ya yi abin da yake daidai, ya kiyaye dokokina sosai, lalle zai rayu.

20. Wanda ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba, mahaifi kuma ba zai ɗauki hakkin laifin ɗansa ba. Adalcin adali nasa ne, muguntar mugu kuma tasa ce.

21. “Amma idan mugu ya bar dukan muguntarsa da ya aikata, ya kiyaye dokokina, ya bi shari'a, ya yi abin da yake daidai, zai rayu, ba zai mutu ba.

22. Ba za a bi hakkin laifin da ya aikata ba. Zai rayu saboda adalcin da ya yi.

Karanta cikakken babi Ez 18